Sojoji sun ceto mutane 6 daga cikin ɗaliban jami’ar Gusau da aka sace

Sojoji sun ceto dalibai mata shida daga cikin daliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau da aka bada rahoton yan bindiga sun yi garkuwa da su a, Zamfara.

Wasu dalibai da ba a san yawansu ba ne aka bada rahoton yan bindiga sun sace daga gidajen kwanansu dake Sabon Gida a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

A wata sanarwa, Sulaiman Idris babban mataimaki na musamman kan kafafen yaɗa labarai ga gwamnan Zamafara ya ce sojojin sun kuma kashe da yawa daga cikin yan bindigar a musayar wuta.

Idris ya ce gwamnan jihar Dauda Lawal Dare ya kirawo taron dukkanin hukumomin tsaro domin tattauna batun sace mutanen.

More from this stream

Recomended

Kotun Tarayya Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa lamarin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa. Mai […]