An yi hasarar rayuka 6 a wani mummunan haÉ—arin mota a hanyar Kaduna zuwa Zaria

Rahotanni sun nuna mutane 6 sun mutu yayin da 11 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen jihar Kaduna, Kabir Nadabo, ya ce hatsarin ya afku ne a tashar Aliko da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya a ranar Talata da misalin karfe 06:25 na safe.

Nadabo ya alakanta yawaitar haÉ—urran da suka yi da yin tukin ganganci, lamarin da ya janyo dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wani dan lokaci.

Sai dai ya ce hanyar a halin yanzu babu walwala da zirga-zirga, inda ya ce tawagar masu aikin ceto na Zebra 35 Rigachikun sun kai dauki cikin gaggawa inda suka kai dauki.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Wasu É—aliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karÉ“ar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...