An samu rabuwar kai tsakanin jam’iyyun adawa kan zaÉ“en shugaban majalisar wakilai

ZaÉ“aÉ“É“un Æ´an majalisar wakilai ta tarayya da aka zaba karkashin jam’iyyun adawa wandanda suka yi wa kansu laÆ™abin ‘Greater Majority’ a turance yanzu haka kansu ya rarrabu kan yan takarar shugaba da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Ƙungiyar Greater Majority na da mambobi da suka fito daga jam’iyyun adawa 7 a majalisar wakilai ta 10 da ake shirin kafawa.

Jam’iyun sun haÉ—a da PDP, Labour Party(LP) APGA, NNPP, YPP,SDP da kuma ADC.

Ƙungiyar sun gudanar da taruka biyu a lokaci guda a otal ɗin Transcorp Hilton da kuma Frazier Suites dake Abuja a daren ranar Litinin domin lalubo mafita akan lamarin.

Amma kuma tarukan sun fito da mabanbantar matsaya a yayin da É“angare É—aya ya goyi bayan É—antakar sulhu na jam’iyyar APC, Hon Tajuddeen Abbas(APC Kaduna)da Benjamin Kalu(APC Abia) a matsayin shugaba da mataimaki.

A karshen kammala taron na otal É—in Transcorp Hilton wata sanarwa mai É—auke da sahannun sakataren taron, Kabiru Alahsan Ruwa da kuma shugaban taron Idu Igariwey ta bayyana cewa sun yanke shawarar haÉ—e kan su domin goyon bayan Abbas.

Amma kuma a taron da aka gudanar a otal É—in Frazier Suites, Victor Afam Ogene wanda ya bayyana matsayar taron ya ce ba su da wani takamaiman É—an takara da suke goyon baya tun da babu wanda ya tsaya takarar daga jam’iyyun adawa.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...