‘Yan majalisar dattawa sun nemi sojoji su datse hanyoyin da barayin daji suke tserewa

0

‘Yan majalisar dattawan Najeriya sun umarci sojoji da sauran jami’an tsaron kasar da su sanya ido sosai tare da datse hanyoyin da ‘yan ta’adda da barayin daji ke bi suna tserewa domin hana su komawa wasu sassan kasar.

Majalisar ta bayar da umarnin ne bayan gabatar da kuduri da mataimakin Gagarabadau, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, na jihar Neja ya yi sakamakon sabbin hare-hare da satar mutane da ake yi a yankunan kananan hukumomin Mariga da Mashegu da Kontagora da kuma Borgu na jihar Naija.

Sanatan ya ce sakamakon muggan hare-haren da sojoji da sauran jami’an tsaro ke kai wa ‘yan ta’adda da barayin daji da suka addabi yankunan gabashin jihar Sokoto da Zamfara, ‘yan ta’adda na ta tserewa suna shiga jihar Naija.

A don haka ya ce ya kamata a tsara hare-haren da ake kai wa ‘yan ta’addar da kyau yadda ya kamata ta yadda za a datse duk wata hanya da suke bi suna guduwa suna shiga sassan jihar Naija.

Majalisar kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito ta kuma umarci hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya da ta samar da kayan abinci da sauran muhimman abubuwa na jin dadi ga mutanen kauyukan da hare-haren ‘yan ta’addar ke shafa da kuma ‘yan gudun hijira a yankunan kananan hukumomin Mariga da Mashegu da Kontagora da kuma Borgu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here