Sojoji Sun kashe Mayaƙan Boko Haram 3 Tare Da Ceto Mutane 9

Dakarun sojan Najeriya na rundunar, Operation Haɗin Kai sun kashe mayaƙan Boko Haram uku a ƙaramar hukumar Bama dake jihar Borno.

A cewar Zagazola Makama wani masani dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce an kashe mayaƙan ne lokacin da sojoji suke gudanar da aikin sintiri.

Ya ce an kashe ƴan ta’addar ne a ƙauyen Churchur a yayin musayar wuta lokacin da sojojin suke sintiri.

A wani farmakin na daban sojojin sun samu nasarar ceto mutane 9 da suka haɗa da mata uku da ƙananan 6 s sun kuma lalata sansanin mayaƙan na Boko Haram bayan da suka tsere.

Hakan na zuwa ne ƴan kwanaki bayan da sojoji suka kashe wasu mutane uku a wani samame da suka kai maɓoyar Boko Haram da kuma mayaƙan ISWAP a jihohin Borno da Katsina

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...