Sojin Najeriya Ta Karbi Korafi Sama Da 500 Na Zargin Cin Zarafin Mutane Da Sojoji Suka Yi wa Farar Hula

ABUJA, NIGERIA- A wani yunkuri na inganta dangantakarta da al’ummar kasa, rundunar sojin Najeriya karkashin sashin harkokin farar hula na rundunar ta bayyana cewa sojin kasar ta samu rahotanni tare da daukar matakai akan korafe karafen take hakkin dan’adam sama da 500 da jami’anta suka yi cikin shekaru 6.

Hakan na zuwa ne yayin wata ganawa da sashin ya yi da ‘yan jaridu kan kulla kyakyyawar dangataka da kafofin watsa labarai don taka rawa wajen magance matsalolin tsaro a kasar.

A baya dai wasu kungiyoyin kare hakkin dan’ adam irin su Amnesty International da ‘yan Najeriya sun sha zargin rundunar soji kasar da cin zarafin farar hula, batun da Shugaban sashin harkokin farin hula na rundunar sojin kasar Manjo Janar Markus Kangye ya yi karin haske game da wannan bangare da ke karkashin sashinsa wanda ke kula da korafe-korafen farar hula kan sojin kasar.

jami'an sashin harkokin farar hular sojin Najeriya
jami’an sashin harkokin farar hular sojin Najeriya

“An kafa wannan bangare domin magance take hakkin bil’adama da ake zargin sojoji da aikatawa a lokacin ayyukansu na tsaron cikin gida da yaki da ta’addanci da ta da kayar baya a Najeriya, wanda a cewar ya kasance wani muhimmin ci gaba da aka samu tun daga shekarar 2016.”

Ya kuma kara cewa sai an yi kwakkwaran bincike kan dukkan korafe-korafe da ake samu, kuma a lokuta da dama wasu na da inganci yayin da wasu ba su da shi

Alkaluman da sashin ya bayar sun yi nuni da cewa an samu nasarori a korafe-korafe kan jami’an sojin kasar bisa zargin take hakin dan adam, lamarin da aka danganta da yawan tarukan wayar da kan jama’a kan sanin tasirin wannan bangare na sashin farar hula na rundunar sojin Najeriya.

Birgediya janar Ojogbane Adegbe, Daraktan a fannin ayyukan sanin halayan dan Adam na sashin ya ce “sojojin da muke turawa ko suke aiki a bangaren ba sa saka kayan aiki, don muna son jama’a da suke da wani korafi kan jami’an mu su iya zuwa ba tare da sun ji tsoro ba kuma duk wanda ya je wajen ba zai gane cewa jami’an soji ba ne amma dukkan masu aiki a wajen sojoji ne.”

Jami'an sashin harkokin farar hular sojin Najeriya da yan' Jaridu
Jami’an sashin harkokin farar hular sojin Najeriya da yan’ Jaridu

Sanin muhimmacin rawar da kafafen watsa labarai ke takawa wajen magance matsalar tsaro musaman ma ga yadda jami’an tsaron suke gudanar da ayyukansu, ya sa sashin farar hula na sojin kasar bullo da dabarun inganta dangataka dake tsakani kamar yadda tsohon Birgediya Janar Usman kuka sheka ya ba shawara

Wannan dai shi ne kwatan farko da sashin farar hula na rundunar sojin kasar ke irin taron karawa juna sani da kafafen watsa labarai don inganta dangantaka al’umma farar hula da rundunar soji kasar.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...