Rundunar Sojin Najeriya Ta Nisanta Kanta Daga Karbar Mulkin Kasar

Wani babban lauya a kasar Robert Clarke ne, ya shawarci shugaba Muhammadu Buhari da ya mika mulki na dan lokaci ga rundunar sojin kasar, domin ta samar da maslaha akan dimbin matsalolin tsaro da tattalin arziki da suka yi wa kasar katutu.

A yayin da yake tsokaci a gidan talabijin na CHANNELS, Clarke ya ce sha’anin tabarbarewar tsaro ya kai halin la haula a kasar, ta yadda “soja ne kadai za su iya magance wadannan matsalolin a halin yanzu.”

Clarke, wanda ya ce Najeriya ta kama turbar wargajewa sakamakon rashin tsaro, ya bayyana cewa kamata yayi soji su karbi iko na wuccin gadi, su kuma mayar da kasar bisa tsarin jihohi 6 kamar yadda ta taba zama a can baya.

Babban Lauya Robert Clarke
Babban Lauya Robert Clarke

A cewar babban lauyan, shugaba Buhari na da karfin iko a karkashin kundin tsarin mulki na 1999, da zai mika mulki na dan lokaci ga rundunar soji, tare da dora mata nauyin mayar da kasar a tsarin na jihohi 6 domin daidaita al’amura.

“Kasar nan na bukatar dokar ta baci. Kamata yayi shugaba Buhari ya tattauna da ‘yan majalisun dokoki na tarayya da na jihohi da kuma gwamnoni akan saka dokar nan take,” in ji lauya Clarke.

To sai dai da take maida martani akan wannan batu, rundunar sojin kasar ta ce za ta ci gaba da tsayuwa kaimun kan biyayya ga gwamnati mai ci yanzu, da kuma dukkan tanade-tanaden mulkin dimokaradiyya.

A wata sanarwa daga Daraktan watsa labarai na rundunar tsaro, Janar Onyema Nwachukwu, ta ce rundunar “za ta ci gaba da kauracewa siyasa, goyon bayan gwamnatin farar hula, da kuma da’a da biyayya ga shugaban kasa da kuma kundin tsarin mulkin kasa.”

Shugaban Najeria Muhammadu buhari Tare da manyan hafsoshin tsaro
Shugaban Najeria Muhammadu buhari Tare da manyan hafsoshin tsaro

Nwachukwu ya kara da cewa sojin kasar za su ci gaba da aiwatar da ayukansu bisa kwarewa, na kare martabar dimokaradiyya da mutuncin kasa, kazalika da kuma tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Don haka sanarwar ta gargadi ‘yan siyasa da ke ruruta wutar rikicin neman hambarar da gwamnati ta haramtacciyar hanya da su shiga taitayinsu, domin kuwa rundunar sojin a tsaye take wajen kare dimokaradiyya.

Ta kuma tunatar da dukkan jami’an sojin kasar cewa babban laifi ne su ma yi tunanin tsunduma a wannan keta dokar, inda kuma ta sha alwashin hukunta duk wani jami’in soji da ya yarda ya karbi hudubar irin wadannan ‘yan siyasar.

Buhari Ya Jagoranci Taron Tsaron Kasa Tare Da Manyan Shugabannin Hukumomin Tsaron Najeriya
Buhari Ya Jagoranci Taron Tsaron Kasa Tare Da Manyan Shugabannin Hukumomin Tsaron Najeriya

Duk da yake sanarwar ta tabbatar da cewa kasar na cikin wani mawuyacin hali, to amma ta ce tana hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin samo bakin zaren warware matsalolin, tare da baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa “al’amura za su daidaita nan ba da jimawa ba.

A baya-bayan nan dai, Najeriya ta rasa sojoji da dama a yayin da suke aikin tsaron kasa sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram a yankunan arewa maso gaba musamman jihohin Borno da Yobe.

Haka ma wani shugaban dakarun sojojin kasar da wasu manyan jami’ai bakwai sun mutu a lokacin da ‘yan Boko Haram suka kai wani hari a jihar Borno a baya-bayan nan.

Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro a kusan dukannin yankunan ta kama da mayakan Boko Haram a yankunan arewa maso gabas, ‘yan bindiga dadi da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a arewa maso yamma, ayyukan tada zaune tsaye na haramtaccen kungiyar IPOB, mai fafutukar kafa kasar Biyafara, a kudancin kasar, da dai sauran su.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar ƙera bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...