Rikici kan abinci ya sa wani magidanci kashe matarsa.

Yan sanda a jihar Edo sun kama wani mutum mai suna, Salami Anedu ɗan shekara 21 kan zargin kashe matarsa sakamakon saɓani sa suka samu akan abinci.

Mutumin da ake zargi na daga cikin jerin masu laifuka da rundunar yan sandan jihar ta kama kuma ta gabatarwa da manema labarai su.

Mai magana d yawun rundunar, SP Chidi Nwabuzor ya ce ofishin yan sanda na Fugar ne suka kama mai laifin a ranar 30 ga watan Agusta.

Ya ce wani mutum mai suna, Aluaye Momoh a ranar 29 ga watan Satumba ya kai kara wurin yan sanda cewa wani mutum Salami Anedu yayi amfani da sanda ya kashe matarsa, Esther Friday mai shekaru 21 a gidansu dake kauyen Ugbekpe a jihar Edo kan sabani da suka samu akan al’amuran gida.

Mai magana da yawun rundunar ya ce wanda ake zargi ya daki matarsa da katako a lokacin saɓanin inda kuma hakan ya yi sanadiyar ajalinsa.

Sai dai Salami ya musalta aikata kisan kan inda ya ce matar tasa dama bata da lafiya kafin rikicin na su kuma ta mutu ne a gidansu.

More from this stream

Recomended