
Wata mata mai ƴaƴa shida ta kashe kanta bayan da ta rataye kanta da zani a banɗaki.
Lamarin ya jefa al’umma cikin ruɗani ya faru ne a garin Warri dake karamar hukumar Warri South ta jihar Delta.
Marigayiyar wacce ta haura shekaru 70 a duniya ta fito ne daga masarautar Olumo dake karamar hukumar Ughelli tun da farko an yi zargin tayi kokarin kashe kanta ta hanyar shan guba.
Matar da akewa kallon mai bin addinin Kirista na Cocin Katolika sau da kafa ce ta aiwatar da barazanar kashe kanta ne a cikin banɗakin dake harabar gidan da take zaune.
Jikar matar ce ta lura cewa ta shafe tsawon lokacin da ya wuce ƙa’ida a banɗaki a bin da ya sa ta nemi a kawo musu ɗauki kuma aka gano gawarta.