Rikici kan abinci ya sa wani magidanci kashe matarsa.

Yan sanda a jihar Edo sun kama wani mutum mai suna, Salami Anedu ɗan shekara 21 kan zargin kashe matarsa sakamakon saɓani sa suka samu akan abinci.

Mutumin da ake zargi na daga cikin jerin masu laifuka da rundunar yan sandan jihar ta kama kuma ta gabatarwa da manema labarai su.

Mai magana d yawun rundunar, SP Chidi Nwabuzor ya ce ofishin yan sanda na Fugar ne suka kama mai laifin a ranar 30 ga watan Agusta.

Ya ce wani mutum mai suna, Aluaye Momoh a ranar 29 ga watan Satumba ya kai kara wurin yan sanda cewa wani mutum Salami Anedu yayi amfani da sanda ya kashe matarsa, Esther Friday mai shekaru 21 a gidansu dake kauyen Ugbekpe a jihar Edo kan sabani da suka samu akan al’amuran gida.

Mai magana da yawun rundunar ya ce wanda ake zargi ya daki matarsa da katako a lokacin saɓanin inda kuma hakan ya yi sanadiyar ajalinsa.

Sai dai Salami ya musalta aikata kisan kan inda ya ce matar tasa dama bata da lafiya kafin rikicin na su kuma ta mutu ne a gidansu.

More News

Ƴan bindiga sun sace wasu É—aliban jami’a biyu a Taraba

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai biyu na Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Wukari a jihar Taraba. A cewar rahotanni ƴan bindigar sun farma wani...

ÆŠalaibai 200 gini ya ruguzo kansu a Jos

Ɗalibai kusan 200 ne suka maƙale cikin ɓaraguzan ginin makarantar da ya rufta da safiyar ranar Juma'a a garin Jos a cewar kwamishinan yaɗa...

An fargabar gini a rufta da dalibai da dama a Jos

Wani gini mai hawa biyu na makarantar Saint Academy da ke Jos ya ruguje, inda dalibai da dama ake fargabar abin ya rutsa da...

Ƙungiyar ƙwadago ta dage sai anbiya 250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gamayyar kungiyoyin ƙwadago za su sake ganawa da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu a cikin kwanaki bakwai domin cigaba da tattaunawa kan mafi ƙarancin...