Mutum 78,000 ne suke mutuwa saboda cutar jeji duk shekara a Najeriya—ƙungiyar likitoci

Kungiyar Likitocin Radiation da Clinical Oncologists ta Najeriya (ARCON) ta ce aƙalla mutane 78,000 ne ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar daji a duk shekara a fadin tarayya.

Yayin da ta kuma nuna rashin jin dadin yadda ‘yan Najeriya ke da lafiyarsu, hukumar ta gabatar da cewa alkaluman da aka gudanar a halin yanzu sun nuna cewa kimanin mutane 125,000 ne ake samun rahoton bullar cutar a duk shekara a kansu a kasar.

Shugaban kungiyar, Dokta Amaka Lasebikan, wanda ya yi jawabi ga manema labarai jiya a Enugu, gabanin taronsu na kimiyya da za a fara daga yau, ya bayyana cewa, matsalar ciwon daji a Najeriya na karuwa, don haka akwai bukatar gwamnati, daidaikun mutane da masu bayar da lafiya su tashi tsaye don magance matsalar.

Ƙungiyar ta ɗaura laifin rashin daidaiton samun kulawar cutar kansa, wanda a cewarta, ya fallasa majinyata da dama ta fuskar bambance-bambancen zamantakewa da tattalin arziki.

More from this stream

Recomended

Kotun Tarayya Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa lamarin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa. Mai […]