Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Naɗa Masu Bada Shawara 20

Majalisar Dattawa a ranar Talata ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya naɗa masu bashi shawara su 20.

Shugaban majalisar, Ahmad Lawan shi ne ya gabatar bukatar shugaban ƙasar dake cikin wata wasikar da ya aikewa majalisar.

Bayan karanta wasikar, Sanata Ibrahim Gobir mai wakiltar mazabar Gabashin Sokoto ya bukaci majalisar da ta amince da bukatar shugaban ƙasar.

Kudirin na Gobir ya samu goyon bayan shugaban marasa rinjaye na majalisar Sanata Philip Aduda.

Majalisar Dattawan ta bawa kudirin kulawar gaggawa inda ta amince da bukatar nan take.

Join Us
  • Facebook38.5K
  • X Network32.1K
  • Behance56.2K
  • Instagram18.9K
Deal Of The Month

    Stay Informed With the Latest & Most Important News

    Loading

    Signing-in 3 seconds...

    Signing-up 3 seconds...