Kotu ta jingine dakatarwar da aka yiwa Kwankwaso daga jam’iyar NNPP

Wata babbar kotu dake Kano ta jingine dakatarwar da aka yiwa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyar NNPP.

Da yake yanke hukuncin a ranar Talata alkalin kotun mai shari’a, Usman Naabba ya kuma hana mambobin jam’iyar tsagin da suka dakatar da Kwankwaso ayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyar NNPP.

A makon da yawuce ne kwamitin amitattun jam’iyar ta NNPP ya ayyana dakatar da Kwankwaso daga jam’iyar kan zargin cin amanar jam’iyar.

Amma kuma wani tsagin jam’iyar dake biyayya ga tsohon gwamnan ya janye dakatarwar da aka yi masa.

Har ila yau kotun ta umarci hukumar zabe ta INEC da kada ta yi aiki da dakatarwar har sai an gama sauraren shari’ar.

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan YaÆ™i Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin Æ™wazon jagorancinsa wajen yaÆ™i da ta’addanci da magance matsalar tsaro a Æ™asar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiÆ™a da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]