Juyin mulki: Najeriya ta rufe iyakokinta da Nijar

A ranar Juma’ar ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba da umarnin rufe dukkan iyakokin kasar da jamhuriyar Nijar cikin gaggawa sakamakon juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan da kuma tashe-tashen hankulan siyasa da ake fama da su a kasar.

A cewar Bashir Adeniyi Adewale, mukaddashin Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCoS), wannan mataki na da matukar amfani ga kasashen biyu.

Gwamnatin tarayya ta umurci masu ruwa da tsaki kan harkokin kula da kan iyakokin kasar da su bada tabbacin cikakken bin wannan umurni, a cewar Adewale, wanda ya je kan iyakar Jibia a jihar Katsina domin sa ido kan matakin da aka dauka.

An ambato Mista Adeniyi yana cewa, “Kamar yadda muka sani, shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu ya kasance mai fafutukar hada kan tattalin arziki a yammacin Afirka. Ya yi imanin cewa kasuwanci da makwabtanmu zai iya kawo ci gaba ga ‘yan Najeriya da sauran jama’ar yankin.”

More from this stream

Recomended