Gwamnatin Zamfara Ta Dauƙe Wasu Motoci A Matawalle

Gwamnatin jihar Zamfara ta kwato wasu daga cikin motocin da ake zargin tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle da yin awon gaba da su lokacin da yabar mulki.

Wasu majiyoyi sun fadawa ji jaridar Daily Trust cewa an kwace motocin ne a yayin wani samame da aka kai gidan tsohon gwamnan dake rukunin gidajen gwamnati a Gusau babban birnin jihar a ranar Juma’a.

Jaridar bata iya gano yawan motocin da aka samu ba sai da sai wata majiya ta ce motoci huɗu kirar Jeep aka samu a gidan.

Jami’an yan sanda ne suka yi dirar mikiya a gidan tsohon gwamnan da bashi da nisa da gidan gwamnatin jihar.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...