An halaka mutane 15 a Burkina Faso | Labarai

Bayanin kashe-kashen ya fito sun fito ne a ranar Talata amma acewar wani shugaban siyasa da ya bukaci kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, ya sakaya sunansa, tun a ranar Litinin da daddare ‘yan bindigar suka kai samamen a wasu kauyukan yankin Seytenga na kasar. Jami’in ya ce ‘yan bindigar sun fara kashe mutane 10 a kauyen Yatakou sannan sai suka matsa kauyen Sofokel inda suka halaka mutum biyar.

Jami’an tsaron Burkina Fason sun tabbatar da labarin, sai dai ba su bayar da adadin mutanen da ‘yan bindigar suka halaka ba. Tuni ma dai hukumomi suka tura da karin jami’an tsaro amma kuma duk da haka lamarin ya sanya mutanen yankin na Seytenga kaurace wa gidajensu.

Wadannan kashe-kashe dai na zuwa ne a yayin da aka sanar da kashe wasu Turawa ‘yan jarida guda uku a Burkina Faso a wani hari da aka kai wa wata tawagar masu gangamin yaki da farautar dabbobi a cikin dazuka.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...