Burkina Faso ta sanya hannu da Rasha kan yarjejeniyar kan gina tashar wutar lantarki ta nukiliya

Shugaban mulkin soja na kasar Burkina Faso yasa ka hannu kan wata yarjejeniya da kasar Rasha ta gina tashar wutar lantarki ta makamashin nukiliya domin inganta samar da wutar lantarki a ƙasar.

Saka hannun na zuwa ne biyo bayan tattaunawa tsakanin Ibrahim Traore da shugaban kasar Russia Vladimir Putin a cikin watan Yuni a wurin taron kasashen Africa-Russia.

A wurin taron Traore ya roki ƙasar Rasha da ta gina tashar wutar lantarki ta nukiliya a kasar Burkina Faso wanda ya ce za ta taimaka wajen samar da wutar da kasar ke bukata.

Traore ya ƙwaci mulki ne a watan Satumba na shekarar 2022 kuma tuni ya mayar da hankali wajen kulla alaka da kasar Rasha domin samun tallafin tsaro da kuma na tattalin arziki.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...