Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan da muke ciki.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne dai-dai lokacin da ake cigaba da fuskantar matsanancin ƙarancin man fetur a sassan ƙasarnan daban-daban.

MEMAN ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata.

“Mambobin mu dake Apapa da kuma sauran wurare dake Lagos sun fara karɓar mai daga jiragen ruwa guda 8 dake ɗauke da litar man fetur sama da miliyan 300 fiye da yadda muka saba karɓa a baya,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ce mambobin ƙungiyar za su tsawaita lokacin aikinsu domin tabbatar da  an loda isassun mota da za su wadata ƙasa da isasshen man fetur.

Ƙungiyar ta MEMAN ta ce kungiyar Direbobin Tankar Mai (PTD) da kuma ƙungiyar NARTO ta masu motocin sufuri sun tabbatar da za su bada goyon baya wajen ganin man ya isa gidajen mai cikin sauri.

More from this stream

Recomended