Sojojin Burkina Faso sun boye gawarwakin farar hula – HRW

BBC
Image caption

Wani sojan Burkina Faso

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta fitar, ya ce an gano gawawwakin mutane dari da tamanin a kaburburan arewacin Burkina Faso inda sojojin gwamnati ke yakar masu tayar da kayar baya.

Kungiyar ta ce akwai hujjojin da suka nuna cewa sojojin ne suka kashe su.

An rika binne mutane ashirin ashirin, a mabanbantan kaburburan da aka hako a kasan gadoji, da filaye da kuma manyan titunan da ke kusa da garin Djibo.

Kungiyar ta bukaci gwamnati ta gano wadanda suka mayar da yankin abin da ta kira ‘Dandalin kashe-kashe’.

Sai dai ministan tsaron Burkina Faso Moumina Cheriff, ya ce kungiyoyin ‘yan bindiga da ke sanye da kayan soji wajen kai hare-hare na iya zama abin zargi.

Karanta wasu labaran

Karuwar matsalar tsaro a Burkina Faso

Image caption

Shugaba Marc Christian Kaboré

Karuwar matsalar tsaro a Burkina Faso

Burkina Faso ta zamo kasa a nahiyar Afrika ta baya bayan nan da ke fuskantar haren haren yan bindiga da ke da nasaba da tsatstsauran ra’ayin addini daga wasu kungiyoyi.

Masana na ganin cewa hare-haren ta’addanci na karuwa ne a yammacin Afrika saboda rashin samar da isasshen tsaro daga kasashen.

Gwamnatin kasar na fuskantar matsin lamba a kan ta dauki sabbin matakai na kawar da ‘yan ta’adda.

A watan Janairun 2020 kadai, an kashe mutum a kalla 60 a wasu hare-hare hudu da aka kai a karo daban-daban a arewacin kasar.

Hare-haren masu tayar da kayar bayan wadanda ke da alaka da kungiyar al-Qaeda da IS, sun karu a shekarar da ta wuce, lamarin da ya tursasawa mutane fiye da rabin miliyan barin gidajensu.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...