An Ceto Malamai Uku  Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara

Sulaiman SaadArewa22 minutes ago

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta sanar da ceto mutum uku daga cikin malamai shida da aka yi garkuwa da su a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Muhammad Bello, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Juma’a.

A ranar 12 ga Satumba, wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da malaman addinin Musulunci shida a kan hanyar Dakko zuwa Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura ta jihar Zamfara.

An ce malaman suna kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara lokacin da ’yan bindigar suka tare motarsu suka sace su.

Kakakin rundunar ’yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun yi kwanton bauna a kan hanyar ne kafin su sace mutanen shida.

Rahoton NAN ya ce malaman suna kan hanyarsu ta halartar wata addu’a ta musamman domin neman taimako da jagorancin Allah ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

An kuma ruwaito cewa masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa har naira miliyan 30 domin sakin su.

Da yake zantawa da manema labarai, Bello ya ce haɗin gwiwar da aka yi tsakanin Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA), Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), da rundunar ’yan sanda ne ya haifar da nasarar ceto malaman.

Kwamishinan ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike da farautar sauran ’yan bindigar tare da ƙoƙarin ceto malamai uku da har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane.

Wani babban jami’in tsaro da ya shiga aikin ceto ya shaida wa NAN cewa an kubutar da malaman ukun cikin ƙoshin lafiya ba tare da sun ji rauni ba.

Ana sa ran za a miƙa malaman da aka ceto ga gwamnatin jihar Zamfara.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...