

Shugabannin jam’iyyar PDP na ƙananan hukumomin Kwami da Nafada dake Jihar Gombe sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Wadanda suka sauya sheƙar sun haɗa da Alhaji Idris Abubakar Yayayi na Kwami da kuma Alhaji Yusuf Isa Jigawa na Nafada. Sun koma APC ne a hukumance bayan wata ganawa a lokuta daban-daban da su ka yi da gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya
Bayanin sauya shekar ta su na kunshe ne cikin wata sanarwa da darakta janar na harkokin yaɗa labarai na gidan gwamnatin jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli,ya fitar.
A cewar sanarwar, ganawar ta samu ne ta hanyar jagorancin Sanata Usman Bayero Nafada wanda shi ne ke rike da mukamin babban jamiin tsare-tsare na kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyar APC a jihar Gombe .
Misilli ya ce tsoffin shugabannin PDP ɗin sun miƙa takardun murabus dinsu ga shugabannin jam’iyyar a mazabunsu, wanda hakan ya kawo ƙarshen kasancewarsu mambobin jam’iyyar adawa ta PDP.
Ya ƙara da cewa sun yi alƙawarin kawo dukkanin tsarinsu na siyasa, hanyoyin yaɗa tasiri a tsakanin jama’a, dabarun tattara magoya baya da kuma mabiya su zuwa APC domin ƙarfafa jam’iyyar a yankunansu.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa yayin da suka gana daban-daban da gwamnan, tsoffin jiga-jigan PDP ɗin sun yabawa salon jagorancinsa tare da bayyana aniyarsu ta ba da gudummawa wajen bunƙasa APC da ƙarfafa damar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.
Yayin da yake karɓar su cikin APC, Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna kwarin gwiwa cewa shigowarsu jam’iyyar zai ƙara ƙarfafa tsarinta na siyasa a Kwami da Nafada tare da faɗaɗa goyon bayan da take samu daga ƙasa.
Gwamnan ya kuma bayyana fatan cewa kwarewarsu ta siyasa, tasirinsu da kuma ƙwarewarsu wajen tattara magoya baya za su ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a ƙoƙarinta na tabbatar da matsayinta a faɗin jihar.
Misilli ya ce wannan ci gaba yana nuna yadda amincewar jama’a ke ƙaruwa ga jagorancin gwamna Inuwa Yahaya da APC a Jihar Gombe yayin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin babban zaɓen shekarar 2027.