

‘Yan majalisar dokokin jihar Zamfara takwas da suka yi murabus daga jam’iyyar APC na shirin komawa jam’iyyar bayan sun gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cewar wata sanarwa da Ahmad Dan-Wudil, mai taimaka wa tsohon gwamnan Zamfara kan harkokin yaɗa labarai, ya fitar a ranar Litinin, Bello Matawalle, ƙaramin ministan tsaro, ne ya jagoranci ‘yan majalisar zuwa ganawar.
Dan-Wudil ya ce a yayin ganawar, ‘yan majalisar sun sake jaddada biyayyarsu da kuma jajircewarsu ga jam’iyyar APC da Shugaba Tinubu.
“Bayan kammala ganawar, Minista Matawalle ya yi alƙawarin haɗa ‘yan majalisar cikin ƙungiyar Tinubu Again Movement, domin su yi aiki tare wajen mara wa Shugaba Tinubu da dukkan ‘yan takarar APC baya a zaɓuɓɓukan da ke tafe.” a cewar sanarwar
Tun farkon wannan wata ne dai ‘yan majalisar suka fice daga jam’iyyar APC, inda suka danganta matakinsu da tabarbarewar tsaro, zargin rashin adalci, da kuma rashin biyan albashi da alawus-alawus.
‘Yan majalisar sun haɗa da:
A wani ɓangaren kuma, kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Bilyaminu Moriki, ya bayyana cewa an riga an dakatar da waɗannan ‘yan majalisa daga ayyukansu tun kafin ficewarsu daga APC.
Moriki ya ce an dakatar da su ne tun ranar 26 ga Fabrairu, 2024, bisa zarge-zargen munanan ɗabi’u a aiki, haɗa baki wajen aikata ba daidai ba, tayar da rikici, nuna rashin girmamawa ga majalisar, da kuma gudanar da zaman majalisa ba bisa ƙa’ida ba wanda ya saɓa wa dokokin majalisar.