
Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun ceto mutane 27 da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina, bayan artabu da wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne.
Jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Danja ya ce dakarun Sector 1 sun samu kiran neman agaji a ranar 16 ga Oktoba bayan rahotannin ayyukan ’yan ta’adda a garin Gamji, inda aka yi garkuwa da mutane 27, maza 15 da mata 12.
Ya bayyana cewa sojojin sun bi sawun maharan ta hanyar Gangare zuwa Kamba, inda suka yi musayar wuta da su. A sakamakon artabun, maharan sun tsere, suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.
A cewar jami’in, an ceto dukkan mutanen 27 ba tare da sun samu rauni ba. Bayan tantance bayanansu, an mika su ga shugabannin al’umma domin sake haduwa da iyalansu.
A wani aikin daban da aka gudanar a wannan rana, dakarun da ke sintiri a kusa da kauyen Kurba, cikin karamar hukumar Kankara, sun ci karo da wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne a kan babura uku.
Danja ya ce wadanda ake zargin sun tsere bayan ganin sojojin, inda suka bar babur daya, wanda dakarun suka kwato.
Ya kara da cewa wadannan ayyuka na daga cikin kokarin rundunar na takaita zirga-zirgar kungiyoyin masu dauke da makamai da kuma kare al’ummomin Arewa maso Yamma.