Ƴan Sanda Sun Kama Mutane Uku Kan Fashi, Kisan Kai Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Bauchi



Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama mutane uku da ake zargi da aikata laifukan fashi da makami, kisan kai da safarar miyagun kwayoyi a wasu samame daban-daban a jihar.

Mai magana da yawun rundunar, SP Nafiu Habib, ya ce an kama Zakariya’u Musa, mai shekaru 22, bisa zargin kwace wayoyin dalibai uku da barazanar wuka a yankin Gidan Gona, Bauchi. An ce wasu abokan aikinsa biyu sun tsere, yayin da ‘yan sanda ke kokarin cafke su.

A wani samame kuma, an kama Isa Moh’d, mai shekaru 20, bisa zargin kashe Salim Moh’d ta hanyar caka masa wuka bayan wani rashin jituwa a ranar 18 ga Oktoba, 2026. Haka kuma, rundunar ta kama Sara Chikodi, mai shekaru 28, bisa zargin safarar miyagun kwayoyi, inda aka samu wasu ganyayyaki da ake zargin tabar wiwi ce da kuma wani sinadarin Methamphetamine a wajenta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya yaba wa jami’an rundunar kan kokarinsu, tare da gargadin masu aikata laifuka da su guji jihar Bauchi.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...