Gwamnatin tarayya ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola a Abuja

Sulaiman SaadHausa23 minutes ago

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da samun wani  mutum ɗaya da ya kamu da cutar Ebola a babban birnin tarayya  Abuja. ministan lafiya Dr Muhammad Ali Pate, ya ce an gano mutane 44 da suka yi hulɗa da mara lafiyar domin a bi sawunsu da kuma hana cutar yaduwa.

A cewar gwamnati, wanda ya kamu da cutar mace ce da ta iso Najeriya daga ƙasar Uganda ta jirgin sama na ƙasa da ƙasa. Matar ta kamu da rashin lafiya a ka kuma kwantar da ita a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja inda ta samu kulawa na wasu kwanaki kafin gwaji ya tabbatar da cewa tana ɗauke da cutar Ebola. A halin yanzu tana cikin killacewa tana karɓar magani.

Hukumar NCDC tare da ma’aikatar lafiya da hukumar lafiya ta birnin Abuja sun fara ɗaukar matakan gaggawa domin dakile yaduwar cutar. An fara bibiyar mutanen da suka yi hulɗa da mara lafiyar, ciki har da ma’aikatan lafiya, marasa lafiya, masu kula da ita da kuma matafiya. Haka kuma an ƙarfafa tsarin sa ido da kariya a asibitin da aka gano cutar.

Gwamnati ta umarci dukkan cibiyoyin lafiya na gwamnati da masu zaman kansu su kasance cikin shirin ko-ta-kwana. An kuma gargadi ma’aikatan lafiya da su gaggauta gano duk wanda ake zargi ya kamu da cutar, su killace shi tare da sanar da hukumomin lafiya cikin sauri.

Ali Pate ya roƙi ‘yan Najeriya su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa cikin lura. Ya tunatar da cewa Najeriya ta yi nasarar shawo kan Ebola a shekarar 2014, yana mai cewa ƙasar na da ƙwarewa da tsarin da za su taimaka wajen sarrafa wannan sabon ƙalubale. Ya kuma bukaci jama’a su bada haɗin kai wajen gano da kuma hana yaduwar cutar.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...