

Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya sanar da rasuwar Reuben Fasoranti, shugaban ƙungiyar siyasa da zamantakewar al’ummar Yarbawa ta Afenifere.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Aiyedatiwa ya bayyana marigayi Fasoranti a matsayin jagora mai daraja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ci gaban Jihar Ondo, yankin Yarbawa da kuma Najeriya baki ɗaya.
“Cikin baƙin ciki ƙwarai amma tare da cikakkiyar miƙa wuya ga nufin Allah, ina sanar da rasuwar babban dattijonmu mai girma, Pa Reuben Famuyide Fasoranti, wanda ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 100 da haihuwa,” in ji gwamnan.
Aiyedatiwa ya bayyana Fasoranti a matsayin “uba kuma jagora, fitilar hikima, gaskiya da kuma hidima ba tare da son kai ba.”
Ya ƙara da cewa shawarwari, kulawar uba da kuma tsayuwar dakar da marigayin ya yi wajen adalci da shugabanci nagari za su kasance abin kewa.
Gwamnan ya kuma ce Fasoranti ya yi rayuwa mai albarka kuma ya bar gadon tarihi da za a ci gaba da tunawa da shi har ya zuwa shekaru masu zuwa.
A madadin gwamnatin Jihar Ondo da al’ummarta, Aiyedatiwa ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Fasoranti, al’ummar Masarautar Akure da daukacin mazauna jihar.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya sa ya huta cikin salama.