Zaratan sojan ruwa na Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 34 a yankin tafkin Chadi

Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya ta ce zaratan dakarun sojan ruwan Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 34 a hare-haren  suka gudanar a yankin Tafkin Chadi.

Abiodun Folorunsho, kyaftin a rundunar sojojin ruwa kuma daraktan yaɗa labarai na rundunar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar. Ya ce an gudanar da hare-haren ne tare da haɗin gwiwar  dakarun Brigade ta 403 na  Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya a ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai.

Ya ce farmaki na farko ya gudana ne a ranar 28 ga Oktoba, shekarar 2026, yayin da na biyu ya gudana a ranar 30 ga Oktoba, 2026.


“A ranar 28 ga Oktoba, 2026, zaratan dakarun   Sojojin Ruwa na Najeriya sun kai hare-hare kan ‘yan ta’adda. Rahotannin farko sun nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda 8 a artabun. Sai dai bayan tantance ɓarnar da aka yi a fagen daga, an sake duba alkaluman inda aka tabbatar da cewa an kashe ‘yan ta’adda 28.” A cewar sanarwar

“A wani farmaki daban da aka kai ranar 30 ga Oktoba, 2026, zaratan dakarun da ke sansanin Sojojin Ruwa na Tafkin Chadi sun kai hari kan wata maɓoyar mayaƙan Boko Haram da aka gano a Dumba.

“Rahoton farko na tantance sakamakon harin ya nuna cewa an kashe kusan ‘yan ta’adda 6, yayin da wasu da dama suka jikkata.

“Har yanzu ana ci gaba da tantance cikakkun alkaluman waɗanda aka kashe ko suka jikkata yayin da ake gudanar da ƙarin binciken sakamakon farmakin.”

Folorunsho ya ce sabuwar rundunar zaratan dakarun  Sojojin Ruwa ta zama  ƙarin ƙarfi  ga rundunar Operation Hadin Kai  tun bayan tura su aikin, inda suka taimaka wajen ƙarfafa hare-haren sojoji a kan ƙungiyoyin ta’addanci.

Ya ƙara da cewa gudummawar da suke bayarwa ta ƙara wa sojoji ƙarfin kai hare-hare kan maɓoyar ‘yan ta’adda, da dakile ayyukansu, tare da hana mayaƙan Boko Haram walwala da motsi a yankin Tafkin Chadi.

Ya kuma ce za a ci gaba da gudanar da irin waɗannan hare-hare domin rage ƙarfin ƙungiyoyin ta’addanci da kuma tallafa wa ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...