
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba ta da wani shiri na sauya jadawalin babban zaɓen shekarar 2027, tana mai cewa za a gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wani taron tattaunawa da ma’aikatan hukumar daga jihohi shida na yankin Kudu maso Kudu, wanda aka gudanar a Fatakwal, Jihar Rivers.
Ya ce hukumar ta riga ta tsara lokacin gudanar da zaɓen bisa tanadin doka, kuma ba za ta sauya shi ba saboda kowane dalili.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu jam’iyyun siyasa ke iƙirarin cewa INEC na shirin ɗage babban zaɓen.
Amupitan ya ce: “Jadawalin da doka ta tanada ya kafu. Ba za mu sauya komai ba. Dole ne a gudanar da zaɓen a lokacin da aka tsara.”
Ya kuma bayyana cewa hukumar za ta ba Jihar Rivers kulawa ta musamman a zaɓen mai zuwa, saboda muhimmancin jihar a yankin da kuma kasancewarta jiha mafi yawan masu rajistar zaɓe a Kudu maso Kudu.
A cewarsa, Rivers na da masu rajistar zaɓe 3,736,434, sai Jihar Delta mai 3,525,988, Edo mai 2,865,263, Akwa Ibom mai 2,566,198, Cross River mai 1,928,978, da Bayelsa mai 1,200,691.
Ya ce jihohin shida na yankin suna da jimillar masu rajistar zaɓe 15,823,550, inda ya jaddada cewa dole ne ma’aikatan hukumar su tabbatar da cewa babu wanda aka hana damar kaɗa ƙuri’a sakamakon gazawar aiki.
Shugaban INEC ya kuma ce hukumar ta wallafa rajistar masu zaɓe a intanet da kuma wuraren da aka ware domin jama’a su duba.
Ya bayyana cewa hukumar ta karɓi sama da buƙatu 5,000 na gyaran bayanai, ciki har da sunaye da ranakun haihuwa, da kuma ƙorafe-ƙorafe sama da 600 da suka shafi rajistar, waɗanda ake ci gaba da tantancewa.
Amupitan ya sanar da cewa hukumar za ta fitar da cikakkiyar rajistar masu zaɓe a ranar 15 ga Disamba, tare da tabbatar da cewa za a warware dukkan matsalolin da suka rage kafin lokacin.
Ya ce hukumar ta yi tunanin sake tantance rajistar masu zaɓe bayan ya kama aiki, amma daga bisani ta yi watsi da shawarar saboda kusancin lokacin gudanar da babban zaɓen.
Dangane da shirye-shiryen gudanar da zaɓe cikin lumana da gaskiya, Amupitan ya ce INEC za ta yi amfani da darussan da ta koya daga zaɓukan gwamnonin da aka gudanar a wasu jihohi a lokutan da ba na babban zaɓe ba, musamman zaɓen Jihar Osun.
Ya ce zaɓen Osun ya samu kaso mafi girma na fitowar masu zaɓe a tarihin zaɓukan gwamna da ake gudanarwa a lokutan daban da babban zaɓe, kuma an yaba da sahihancinsa a cikin gida da ƙasashen waje duk da fargabar tsaro da aka samu a baya.
Ya ce hukumar za ta yi amfani da ƙwarewar da ta samu daga waɗannan zaɓuka wajen inganta shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Game da tsaro, shugaban INEC ya ce hukumar na aiki tare da hukumomin tsaro, ciki har da ’yan sanda da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), domin tabbatar da lafiyar masu zaɓe, ma’aikatan zaɓe da kayayyakin gudanar da zaɓe.
Ya jaddada cewa hukumar ba za ta ƙarfafa wa ’yan Najeriya gwiwar karɓar katin zaɓensu na dindindin (PVC) sannan ta kasa tabbatar da tsaronsu idan sun fito kaɗa ƙuri’a ba.
Haka kuma, Amupitan ya yi watsi da fargabar cewa fasahar basirar ɗan Adam (AI) ko wasu algorithms za su iya tantance sakamakon zaɓen 2027, yana mai cewa ’yan Najeriya ne za su yanke hukuncin sakamakon zaɓen.
Sai dai ya yi gargaɗi kan ƙarin barazanar kutse ta yanar gizo da ke tattare da amfani da AI, inda ya ce hukumar za ta binciki hanyoyin amfani da fasaha wajen kare na’urorinta da tsarin aikinta daga hare-hare.
A ƙarshe, ya gargaɗi ma’aikatan INEC da ma’aikatan wucin gadi, ciki har da waɗanda ke yi wa ƙasa hidima ta NYSC, da su guji duk wani yunƙuri na kawo cikas ga sahihancin zaɓe a wuraren da aka tura su, yana mai cewa za a hukunta duk wanda ya aikata hakan bisa doka.