Yan sanda sun kama ƴan daban da su ka kai wa Sowore farmaki a Ekiti



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ekiti ta bayyana cewa jami’anta sun kama wasu mutane 11 da ake zargi da hannu a harin da aka kai wa Omoyele  Sowore ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC (African Action Congress), da wasu mutane a gidan cin abinci na Tawakalitu da ke yankin Dalimore a Ado-Ekiti.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, kakakin rundunar, Abutu Sunday, ya ce jami’an Rundunar  Kai Ɗaukin Gaggawa ta Musamman da aka fi sani da (RRS) sun kama waɗanda ake zargin da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Juma’a a maboyarsu da ke yankin Atikankan na Ado-Ekiti, babban birnin jihar.

Sanarwar ta ce:

“Waɗanda ake zargin su ne: Joseph Tayo mai shekaru 32, Olatunji Abayomi mai shekaru 41, Isaac Amba mai shekaru 22, Kehinde Ajigbana mai shekaru 18, Tosin David mai shekaru 18, Solomon Iyanu mai shekaru 18, Ogunsola Ayomide mai shekaru 21, Ojo Ayodeji mai shekaru 22, Kayode Dada mai shekaru 32, Segun Olatunji mai shekaru 28, da Salami Emmanuel mai shekaru 53.”

“Kayayyakin da aka kwato a wurinsu sun haɗa da na’urorin sadarwa guda biyu (walkie-talkies), wasu abubuwa da ake zargin tabar wiwi ce da Colorado, injinan markaɗe tabar wiwi guda biyu, fakiti ɗaya na Rizla, katunan ATM guda bakwai, wayoyin hannu guda goma sha uku, mukullan mota guda biyu, faifan adana bayanai (flash drive) guda ɗaya, na’urar Wi-Fi ta MTN mai fasahar 5G guda ɗaya, katunan shaida daban-daban, fasfo ɗin ƙasashen waje guda takwas,  wasu layu biyu da ake zargin na aikata laifuka ne, laita  ta kunna wuta guda ɗaya, da kuɗi Naira 250.”

Sunday ya ce an tsare waɗanda ake zargin domin ci gaba da bincike, yana mai ƙara da cewa ana cigaba da  gudanar da bincike domin gano rawar da kowannensu ya taka a harin, tantance alaƙarsu da juna, da kuma gano sauran mutanen da ka iya kasancewa da hannu a lamarin.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...