Sowore Ya Zargi DSS Da Taimakawa ’Yan Daba Wajen Kai Masa Hari a Ado-Ekiti

Omoyele Sowore, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), ya zargi Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) da taimaka wa wasu “’yan daba da gwamnati ta ɗauki nauyi” wajen kai masa hari tare da tawagarsa a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, ɗan gwagwarmayar ya ce lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan kammala wata hira da ya yi a gidan rediyon Midas FM 90.5 da ke Ado-Ekiti.

Swore ya  “An kai mana mummunan hari tare da jikkata mu daga hannun wasu ’yan daba masu makamai da gwamnati ta ɗauki nauyinsu a Ado-Ekiti, jihar Ekiti.

Hukumar DSS ta ba waɗannan maharan cikakken bayanin inda muke, wanda ya ba su damar aiwatar da wannan mummunan harin. Ba za mu ja da baya ba! Muna da ƙasa da za mu ’yantar.”

A wani saƙon daban, Sowore ya wallafa hotunansa da na ɗaya daga cikin masu taimaka masa suna kwance a gadon asibiti. Ya yi zargin cewa maharan sun fito ne daga Gidan Gwamnatin Jihar Ekiti kuma suna samun goyon bayan DSS.

“Wannan shi ne irin munin halin da Najeriya ta faɗa cikinsa! Waɗanda suka kai mana mummunan hari a Ado-Ekiti yau sun fito ne daga Gidan Gwamnati.

An san su sosai, kuma DSS ne suka samar musu da bayanan bibiyarmu da kuma tallafin gudanar da harin.”

Sowore ya kuma yi zargin cewa jami’an DSS sun kasance suna bibiyarsa tare da cin zarafin tawagarsa tun bayan isowarsu jihar Ekiti a ranar da ta gabata.

“Har ma sun yi wa manajan wurin farko da muka ci abinci barazana, suna gargaɗinsa kada ya sake bari mu yi amfani da wurinsa.” a cewarsa

Ya kuma yi watsi da kalaman Falade Michael, kwamishinan ’yan sanda na jihar Ekiti, wanda ya bayyana lamarin a matsayin “ƙaramar saɓani” kawai.

Sowore ya ce kwamishinan ya kai ziyarar gani da ido zuwa inda aka kai harin kuma ya ga irin munanan raunukan da shi da tawagarsa suka samu.

Ya ƙara da cewa “Kwamishinan ya ga raunukan, ya shaida abin da ya faru bayan harin, kuma ya san girman lamarin sosai.

Amma duk da haka rundunarsa ta zaɓi rage girman harin, har ta bayyana raunukan da muka samu a matsayin ‘ƙanana’.

Ba abin mamaki ba ne yadda ake zargin cewa shi kansa kwamishinan ’yan sandan yana da hannu a lamarin. Wannan abin kunya ne!”

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, DSS ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance domin mayar da martani ga waɗannan zarge-zargen ba.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...