Mutane uku sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota a jihar Kwara

Sulaiman SaadHausa, Arewa44 minutes ago

Akalla mutum uku ne aka bada rahoton cewa sun ƙone ƙurmus bayan wata mota bas da wata babbar mota suka yi karo da juna  sannan suka kama da wuta a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.

An  bayyana cewa haɗarin ya faru ne kusa da gidan mai na Ibrolak, a yankin Okolowo na birnin, a ranar Juma’a.

Shedun gani da ido sun fadi cewa motar bas ɗin tana tafiya ne daga Legas zuwa arewacin ƙasar, yayin da tirakar ke fitowa daga ɓangaren Shao.

Ya faɗawa  wakilin jaridar  Daily Trust cewa , wadda ke ɗauke da buhunan da ake zargin sun ƙunshi dusar katako na ƙoƙarin juyawa zuwa hanyar Okolowo ne lokacin da bas ɗin da ke tahowa ta ci karo da ita.

An ce karon ya haddasa tashin gobara da ta rufe motar bas ɗin gaba ɗaya, lamarin da ya sa mutum uku suka ƙone har ba a iya gane su ba.motar bas ɗin na ɗauke da ƙananan kaji da aka ƙyanƙyashe kwana ɗaya kacal, amma har yanzu ba a tabbatar ko akwai wasu fasinjoji a cikin motar baya ga waɗanda suka mutu ba.

Motar bas ɗin na kuma  ɗauke da ƙananan kaji sabuwar ƙyanƙyasa , amma har yanzu ba a tabbatar ko akwai wasu fasinjoji a cikin motar baya ga waɗanda suka mutu.

Ya ƙara da cewa jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) sun isa wurin da safiyar Juma’a domin kwashe gawarwakin mamatan.

Kwamandan FRSC na Jihar Kwara, Kabiru Babatunde Kazeem, ya tabbatar da faruwar haɗarin lokacin da wakilin jaridar ya tuntube shi.

Ya yi alƙawarin bayar da ƙarin bayani daga baya, amma har zuwa lokacin da ake kammala wannan rahoto bai yi hakan ba, duk da ƙarin kiran da aka yi masa domin samun sabbin bayanai game da lamarin.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...