

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan dakarun rundunar Operation Enduring Peace (OPEP) dake aikin samar da tsaro a jihar Filato a wani shingen binciken ababen hawa da ke ƙaramar hukumar Riyom a jihar Filato inda suka kashe soja guda ɗaya tare da kwashe bindigogi guda biyu.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Juma’a lokacin da dakarun shiya ta 6 na rundunar ta OPEP da ke jibge a Ungwan Boka suka fuskanci hari a wurin shingen binciken
Kafar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi dama sauran sassan Najeriya ta ruwaito daga majiyoyi cewa maharan sun buɗewa dakarun wuta mai ƙarfi daga wurare daban-daban, lamarin da ya sa dakarun suka mayar da martani tare da shiga musayar wuta da su.
An ce bayan musayar wutar, maharan sun ja da baya zuwa cikin dazukan da ke kewaye da yankin.
Sai dai a yayin artabun, wani soja mai muƙamin sajan da ke aiki a asibitin sha ka tafi na rundunar sojan Najeriya da ke Tigi ya rasa ransa. Majiyoyin sun bayyana cewa sojan ya je wurin ne domin wata ziyara ta aiki lokacin da harin ya faru.
Daga baya, an ɗauke gawarsa zuwa ɗakin ajiyar gawa na dake asibitin rundunar sojan Najeriya shiya ta 3.
Rahotanni sun ce an tura ƙarin dakaru da suka fara kai samame domin farautar maharan da kuma ƙoƙarin ƙwato makaman da aka sace.
Wannan ne hari na uku cikin mako guda da aka kai wa jami’an rundunar sojin Najeriya a jihar.