
Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Yakubu Dogara, ya bayyana cewa matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta ba su fara ba ne a lokacin mulkin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ta’addanci, tada ƙayar baya da ’yan bindiga sun daɗe suna addabar ƙasar tun kafin shekarar 2023.
Dogara, wanda shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwa (Chancellor) na Jami’ar Achievers da ke Owo, Jihar Ondo, ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye ɗalibai karo na 16 na jami’ar, inda ɗalibai 836 suka karɓi takardun shaidar kammala karatu a fannoni daban-daban.
Ya ce matsalolin tsaron ƙasar sun samo asali ne daga rashin tsaro a iyakokin ƙasa, yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba, rashin aikin yi ga matasa da kuma yaɗuwar akidun tsattsauran ra’ayi.
A cewarsa, “Rashin tsaro a Najeriya bai fara da wannan gwamnati ba. Wannan ba hujja ba ce ta kare gwamnati, domin gaskiyar magana ba ta buƙatar kariya. Ta’addanci, tada ƙayar baya, ’yan bindiga, garkuwa da mutane da rikice-rikicen al’umma ba su zo Najeriya a shekarar 2023 ba.”
Dogara ya ƙara da cewa matsalolin sun samo asali ne tun shekaru da dama da suka gabata, tun kafin Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023.
Sai dai ya bayyana cewa Tinubu ya sha nuna cewa tsaron ƙasa na daga cikin manyan nauyin da gwamnatinsa ta ɗauka.
Tsohon shugaban majalisar ya kuma taya ɗaliban da suka kammala karatu murna, yana mai cewa Najeriya na buƙatar ƙwarewarsu, fasaharsu da sabbin dabarunsu domin ci gaban ƙasa.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar, Farfesa Bode Ayorinde, ya ce Najeriya ta samu ci gaba wajen faɗaɗa damar samun ilimin jami’a, amma ya nuna damuwa kan irin damar da ke jiran waɗanda suka kammala karatu bayan barin makaranta.
Ayorinde ya ambato alkaluman Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), waɗanda suka nuna cewa Najeriya na da jami’o’i 312 zuwa watan Yunin 2026. Daga cikinsu, 77 na gwamnatin tarayya ne, 67 na gwamnatocin jihohi ne, yayin da 168 mallakar masu zaman kansu ne.
Ya ce waɗannan jami’o’i na wakiltar gagarumin jari a fannin bunƙasa ilimin ɗan Adam, inda iyaye, gwamnatoci da malamai ke sadaukar da albarkatunsu wajen samar da ƙwararrun ma’aikata. Sai dai ya yi tambaya kan irin damar da ke jiran waɗannan ɗalibai bayan kammala karatunsu.
A nata jawabin, Mataimakiyar Shugabar Jami’ar, Farfesa Omolola Irinoye, ta ce tun lokacin da aka kafa jami’ar take ƙoƙarin samar da ingantaccen ilimi wanda ya haɗa da haɓaka tunani, koyar da ƙwarewar aiki, gina ɗabi’a da kuma koyar da ɗaukar nauyin zamantakewa.