
Majalisar Dattawan Najeriya ta fara nazarin buƙatar Shugaba Bola Tinubu na amincewa da karɓar bashin waje na dala biliyan 7.7, kwatankwacin naira tiriliyan 10.79, domin taimakawa wajen gudanar da kasafin kuɗin shekarar 2026.
A zaman majalisar na ranar Laraba, an miƙa buƙatar ga kwamitin da ke kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje domin gudanar da cikakken bincike tare da gabatar da rahoto.
Tinubu ya aika da wasiƙar buƙatar ga shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar 26 ga Oktoba, 2026. A cikin wasiƙar, ya nemi amincewar Majalisar Tarayya domin karɓar bashin da ya kai naira 10,790,366,835,481, kwatankwacin dala 7,707,404,882.49, bisa la’akari da canjin dala ɗaya kan naira 1,400.
Bashin da ake nema wani ɓangare ne na shirin Gwamnatin Tarayya na samun sabon bashin naira tiriliyan 29.2 da aka tanada a cikin dokar kasafin kuɗin 2026.
A cewar wasiƙar shugaban ƙasa, shirin ya ƙunshi karɓar bashin cikin gida na naira tiriliyan 18.4 da kuma bashin waje na naira tiriliyan 10.79 domin taimakawa wajen cike gibin kasafin kuɗin ƙasar da aka kiyasta ya kai naira tiriliyan 31.4.
Tinubu ya ce dokar kasafin kuɗin 2026 ta amince da sabon bashin naira tiriliyan 29.2 domin taimakawa wajen biyan gibin da ke cikin kasafin kuɗin shekarar.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa buƙatar ta yi daidai da tanade-tanaden sashe na 21(1) da 27(1) na dokar kafa Ofishin Kula da Basussuka ta shekarar 2003, waɗanda suka tanadi cewa dole ne Majalisar Tarayya ta amince da shirin karɓar bashin ƙasashen waje.
Ya ce Gwamnatin Tarayya za ta yi la’akari da hanyoyi daban-daban na samun kuɗaɗen, bisa la’akari da kuɗin ruwa, ribar da kowace hanya za ta iya samarwa da kuma lokacin da za a ɗauka kafin samun kuɗin.
Sai dai ya nuna cewa gwamnati za ta fi mayar da hankali kan sayar da takardun bashin Eurobond, saboda ana iya kammala tsarin cikin ɗan lokaci kuma ana iya samun makudan kuɗaɗe ta wannan hanya.
Sauran hanyoyin samun kuɗaɗen da aka ambata sun haɗa da rance mai sauƙin sharudda da na kasuwanci daga hukumomin ƙasa da ƙasa da ƙasashen waje, tallafin kuɗi daga Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), rancen wucin gadi, haɗa rance daga masu zuba jari da kuma karɓar bashi kai tsaye daga cibiyoyin hada-hadar kuɗi na ƙasashen waje.
Tinubu ya kuma bayyana cewa za a tantance ainihin kuɗin ruwa, lokacin biyan bashin da sauran sharudda ne a lokacin da za a kammala yarjejeniyar, bisa yanayin kasuwar kuɗi a lokacin.
Ya ce Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya da Ofishin Kula da Basussuka za su haɗa kai wajen tabbatar da cewa Najeriya ta samu sharuddan bashi mafi dacewa da yanayin kasuwa.
Dangane da yadda za a yi amfani da kuɗaɗen, shugaban ƙasar ya ce za a ware su ne domin gudanar da muhimman ayyuka da shirye-shiryen da aka tanada a kasafin kuɗin 2026.
Ya lissafa tsaro, sufuri, noma, wutar lantarki, ilimi da kiwon lafiya a matsayin muhimman fannoni da za su amfana da bashin.
Tinubu ya kuma ce kuɗaɗen za su taimaka wajen gudanar da shirye-shiryen kasafin kuɗi tare da ƙarfafa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta fara.
Wani dalilin da ya bayar na neman bashin shi ne cewa kuɗaɗen da za a samu a matsayin daloli za su taimaka wajen ƙara yawan ajiyar kuɗaɗen waje na Najeriya. Ya ce Babban Bankin Najeriya (CBN) ne zai karɓi kuɗaɗen a madadin Gwamnatin Tarayya.
A cewarsa, ƙarin ajiyar daloli zai taimaka wajen tallafa wa darajar naira da kuma ƙarfafa matsayin tattalin arzikin Najeriya a hulɗar ƙasashen waje.
Da yake mayar da martani kan buƙatar, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya jaddada muhimmancin gwamnati ta nemi rance bisa sharuddan da za su amfani Najeriya.
Ya yi gargaɗin cewa bai kamata a amince da yarjejeniyar bashi ba tare da an yi nazari sosai kan tasirinta ga tattalin arziki da kuma nauyin da zai rataya a wuyan ƙasar wajen biyan bashin ba.
Akpabio ya ce: “Dole ne mu fita mu nemi mafi kyawun sharudda, ta yadda mai bayar da rancen da mai karɓarsa za su amfana.”
Bayan haka, ya miƙa buƙatar ga kwamitin kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje, inda ya umarce shi da ya gabatar da rahotonsa cikin gaggawa.
Kwamitin ne zai binciki hanyoyin samun bashin da gwamnati ta gabatar, da kuma sharuddan da za a yi amfani da su kafin Majalisar Dattawa ta yanke matsayinta na ƙarshe.
Wannan buƙata ta Tinubu na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan ƙaruwar bashin Najeriya, kuɗaɗen da ake kashewa wajen biyan basussuka da kuma yadda gwamnati ke ƙara dogaro da rance domin cike gibin kasafin kuɗi.
Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta sha bayyana cewa karɓar bashi ya zama dole domin cike gibin kuɗaɗen shiga da kuma gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa, ana ci gaba da tambayar dorewar bashin da kuma ko ayyukan da ake amfani da kuɗaɗen wajen gudanarwa za su samar da ribar da ta dace da kuɗin da aka karɓa.