
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani makaniki mai shekaru 24, Mubarak Muktar, bayan zargin samunsa da wata motar Kia Optima ta shekarar 2014 da aka sace, wadda kudinta ya kai naira miliyan takwas.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Ya ce an sace motar bakar fata ne a ranar 4 ga Oktoba, 2026, bayan matar mai motar ta ajiye ta a wajen asibitin Ziha Health Care da ke unguwar Karkasara, karamar hukumar Tarauni.
Sanarwar ta ce jami’an rundunar sun kama wanda ake zargin a garejin Farm Centre da ke Tarauni a ranar 18 ga Oktoba, inda aka same shi da motar. Binciken farko ya nuna cewa makanikin ne ke kula da motar, yayin da bincike ke ci gaba domin gano yadda ta shiga hannunsa.
Rundunar ta tabbatar da cewa an mayar da motar ga mai ita bayan tabbatar da mallakarta. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya kuma shawarci masu motoci da su rika amfani da amintattun makanikai tare da inganta tsaron motocinsu domin kauce wa sata.