Wike Ya Ce Tinubu Ne Zai Lashe Zaben 2027 A Abuja



Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu goyon baya a babban birnin tarayyar a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Wike ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja, yayin ganawarsa da masu ruwa da tsaki a siyasa daga jam’iyyun APC da PDP a karamar hukumar Abuja Municipal Area Council (AMAC).

Ministan, wanda ke jagorantar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a Abuja da jihar Rivers, ya ce bambancin jam’iyya bai kamata ya hana shugabanni hada kai domin ci gaban kasa ba.

Ya danganta kwarin gwiwarsa da wasu ayyukan gwamnatin Tinubu a Abuja, ciki har da ci gaba da aikin hanyar Apo-Karshi bayan shafe shekaru 16 ba a kammala shi ba, da kuma kafa sakatarorin mata da matasa.

Wike ya kuma kare matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa gwamnatocin baya sun amince da matsalolin tsarin amma ba su dauki matakin cire shi ba.

Ya bukaci masu kada kuri’a da su fito da katin zabe na dindindin (PVC) a ranar zabe domin kada kuri’unsu ga Tinubu da ‘yan takarar jam’iyyarsa.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...