Yan bindiga sun kai hari kan ofishin yan sanda a Kogi

0

Da tsakar daren ranar Juma’a ƴan bindiga suka kai hari kan ofishin shiya na yan sanda dake Eika Ohizenyi a karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi inda suka kashe wani Insifecta Jibril dake bakin aiki.

Wani mazaunin yankin, Mallam Momoh Abubakar ya bayyana cewa maharan sun mamaye ofishin yan sandan da misalin 12:15 na tsakar daren ranar Juma’a dauke da bama-bamai da sauran makamai.

Ya bayyana cewa bom na farko da suka jefa kan ofishin ya yi karar gaske da ta tashi mutane da dama daga bacci a yankin ya kara da cewa bama-baman sun lalata wani sashe na ginin ofishin.

Abubakar ya kara da cewa maharan sun ci karensu babu babbaka inda suka shafe sama da sa’o’i biyu ba tare da wani ɗauki ba daga jami’an tsaro ko kuma mutanen gari.

Ya bayyana cewa jami’in dan sanda ɗaya tilo dake bakin aiki, Jibril wanda aka fi sani da Yellow an kashe shi a harin yayin da aka lalata motar sintiri ɗaya da ofishin yake da ita.

Yan bindigar sun lalata tagogin babban masallacin Eika da kuma na cocin Katolika dake garin.

Tuni kwamishinan yan sandan jihar, Edward Egbuka ya bada umarnin tura karin jami’an tsaro zuwa yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here