Tsoron ƴan bindiga ya sa manoma kwashe amfanin gonar da bai karasa nuna ba a jihar Katsina

Manoma a wasu sassan jihar Katsina sun shiga tsaka mai wuya sakamakon yadda ƴan bindiga suke saka shanu suna lalata musu kayan amfanin gona.

Manoman sun bayyana da zarar kayi korafi ƴan bindiga ka iya harbe mutum nan take.

Rahotanni sun nuna cewa manoman suna kwashe amfanin gonar su duk da cewa bai gama karasawa domin gujewa asara.

Garuruwan da suke ƙaramar hukumar Sabuwa na daga cikin wuraren da lamarin yafi kamari.

Wasu mazauna garin Dugun Mu’azu sun koka kan yadda hukumomi su gaza kawo musu ɗauki kan halin da suka samu kansu a ciki.

More from this stream

Recomended