

Wata Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zamanta a Damaturu ta yanke wa wani mutum mai shekaru 45, Abubakar Musa wanda aka fi sani da Daddy, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe matarsa, Ammi Adamu Mamman..
Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe su ka kama wanda aka yankewa hukuncin a ranar 4 ga watan Janairun shekarar 2024, bayan mutuwar matarsa mai shekaru 42 a gidansu da ke unguwar rukunin gidaje na New Bra-Bra Housing Estate dake Damaturu.
Daga baya an gurfanar da shi a kotu bisa zargin aikata laifin kisan kai.
A cewar bayanin da ‘yan sanda suka bayar, wanda ake tuhumar ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda, inda ya yi ikirarin cewa ya tarar da matarsa an soka mata wuka a wuya yayin da suke barci tare a kan gado ɗaya.
Ya kuma bayyana cewa ya ji matarsa tana ihu, kuma da ya farka sai ya ga an soka mata wuka a wuya tana kuma zubar da jini mai yawa.
Rahoton ‘yan sanda ya ƙara da cewa ya yi ikirarin ya ga wani mutum ɗauke da wuƙa, kuma lokacin da ya yi ƙoƙarin cafke shi, wasu mutum biyu suka zo suka taimaka masa wajen tserewa.
Sai dai bayan sauraren shari’ar, Babban Alkalin Kotun Jihar Yobe mai lamba ta 1, Mai Shari’a G. K. Kaigama ya same shi da laifin aikata kisan kai.
Kotun ta yanke hukuncinta ne a ranar Laraba bayan sauraron shaidun mutum takwas da masu gabatar da ƙara suka gabatar.
Mai Shari’a Kaigama ya yi watsi da roƙon wanda ake tuhumar na cewa ba shi da laifi, yana mai cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da dukkan muhimman abubuwan da suka haɗa da laifin kisan kai kuma sun tabbatar da shari’arsu ba tare da wata shakka mai ma’ana ba.
A yayin da yake kare kansa, ta hannun lauyoyinsa Musa ya dage cewa wasu mutane ne suka kashe matarsa bayan sun kutsa kai cikin gidansu.
Alƙalin ya bayyana cewa wanda aka yanke wa hukuncin yana da damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin cikin kwanaki 30 kamar yadda doka ta tanada.