
Fitaccen jarumin fina-finan Najeriya, Francis Duru, ya rasu yana da shekaru 57 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda iyalansa suka sanar.
Iyalansa sun tabbatar da rasuwarsa ne cikin wata sanarwa da suka wallafa a shafinsa na Instagram da sanyin safiyar Juma’a, inda suka gode wa masoyansa da sauran jama’a bisa addu’o’i da goyon bayan da suka nuna.
“Mu, iyalan Francis Duru, muna sanar da rasuwarsa cikin alhini, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
“Muna godiya da addu’o’inku, kaunarku da fahimtarku. Allah Ya sa ransa ya huta cikin salama. Amin,” in ji sanarwar.
Rasuwar jarumin ta zo ne watanni bayan ya musanta rahotannin da suka bayyana cewa yana fama da wata cuta mai barazana ga rayuwarsa. A watan Yuni, wani bidiyonsa da ya nuna yana cikin rauni ya yadu a kafafen sada zumunta, lamarin da ya jefa masoyansa da abokan aikinsa cikin damuwa.
Daga bisani, Duru ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana bidiyon da aka yada a matsayin kirkirarre kuma mai mugun nufi.
An haifi Francis Duru a ranar 27 ga Yuli, 1969, a kasar Kamaru ga iyayensa ’yan Najeriya daga Jihar Imo. Ya yi karatun firamare da sakandare a Kamaru kafin ya dawo Najeriya domin karatun jami’a.
Ya yi karatun wasan kwaikwayo a Jami’ar Port Harcourt da ke Jihar Rivers, inda ya kammala digiri na farko a fannin fasahar wasan kwaikwayo a shekarar 1996.
Duru ya fara harkar fim a shekarar 1989 a fim din Missing Mark, wanda marigayi Ndubuisi Oko ya shirya. Ya kara samun shahara a shekarar 1995 bayan taka rawar Ahanna a fim din Rattlesnake, wani fim mai hade da tashin hankali da barkwanci da marigayiya Amaka Igwe ta shirya.
A tsawon rayuwarsa ta sana’a, ya samu lambobin yabo da karramawa da dama saboda gudunmawar da ya bayar ga masana’antar fina-finan Najeriya. An kuma nada shi jakadan zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya saboda tasirinsa ga matasa.
A shekarar 2020, ya lashe kyautar gwarzon jarumi a babban matsayi a rukunin fina-finan Igbo a bikin Best of Nollywood Awards, sakamakon rawar da ya taka a fim din Mboputa.
Duru ya auri matarsa, Adokiye, a shekarar 2003, kuma sun haifi ’ya’ya hudu tare. Sai dai iyalan sun fuskanci babban rashi a watan Agustan 2024, lokacin da daya daga cikin ’ya’yansu, Ifeanyi, ya rasu.
Rasuwar Francis Duru ta kawo karshen rayuwar wani gogaggen jarumi wanda ya shafe shekaru da dama yana bayar da gudunmawa ga masana’antar fina-finan Najeriya.