

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zargi ’yan adawa da gwamnatocin da suka gabata da haddasa yunwa da talauci da ake fama da su a Najeriya, yana mai cewa gwamnatinsa na aiki domin gyara shekaru na rashin kyakkyawan tafiyar da tattalin arziki.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Kaduna ranar Asabar, Tinubu ya ce waɗanda ke sukar gwamnatinsa kan matsalolin tattalin arzikin ƙasar su ne suka haifar da waɗannan matsaloli.
“Ina jin ’yan adawa na suna magana kan yunwa da talauci. Amma wa ya haifar da waɗannan matsalolin? Su ne suka haifar da su, kuma mu muna aiki domin kawar da su.” a cewarsa
Shugaban ƙasar ya buƙaci ’yan Najeriya su sake ba shi wa’adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na watan Janairun 2027, yana mai tabbatar musu cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙarfafa abin da ya bayyana a matsayin yunƙurin farfaɗo da tattalin arziki.
A cewarsa, gwamnatinsa ta aza tubalin wadata, ci gaba da samar da damammaki ga ’yan ƙasa, musamman matasa.
“Muna da wadata, daidaito, ci gaba, farfaɗowar tattalin arziki da kuma damammaki ga mutanenmu,” in ji Tinubu, yana watsi da sukar da ake yi daga ’yan adawa.
Ya kuma gode wa al’ummar Kaduna saboda goyon bayan da suka ba shi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, tare da roƙonsu su sake zaɓensa da kuma sauran ’yan takarar APC masu neman mukamai daban-daban.
Tinubu ya ƙara da cewa “Wadatarku tana nan. Makomarku tana hannunku. Yatsunku da za ku sa a kan takardar zaɓe su ne za su yanke hukunci. Ku yi hattara da waɗanda ke son yaudararku,”.
Tinubu ya kuma kare matakin gwamnatinsa na cire tallafin man fetur, yana mai cewa wannan mataki ya zama wajibi domin yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma toshe hanyoyin almubazzaranci a tattalin arziki.
“Abin da ya wuce ya wuce. An riga an kawo ƙarshen tallafin man fetur. Muna aiki domin kawo ƙarshen cin hanci da rashawa, ƙirƙira da jabu a takardun kuɗi, rashin gaskiya da safarar kayayyaki ba bisa ƙa’ida ba,” a cewarsa
Shugaban ya yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta walwala da makomar matasan Najeriya.
Haka kuma, ya yaba wa gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, yana mai cewa suna kawo ci gaba tare da biyan albashin ma’aikata a kai a kai.