Sai doka ta yi aiki game da kisan da aka yi wa Ummita, in ji Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta tabbatar da ganin shari’ah ta yi aikinta a batun kashe Ummukhulthum Sani Buhari, matashiyar da ake zargin wani dan China da aikatawa.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayin wani jawabi a fadar gwamnatin jihar ya ce “Zub da jini (ne, don haka) dole maganar shari’ah ta shigo” kuma sai doka ta yi aikinta.

Ya ce tuni suka sa aka kama mutumin da ake zargi Mista Geng Quanrong, bayan mutane sun damke shi a gidansu marigayiyar ranar Juma’a.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne ran Juma’a da dare, inda Geng Quanrong dan shekara 47 ya kutsa kai gidansu Ummita a unguwar Kabuga cikin karamar hukumar Gwale.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike, inda ta mai da batun zuwa babban sashen binciken manyan laifuka bangaren kisan kai.

Mahaifiyar Ummita, Hajiya Lami Sani Buhari ta ce mutumin da ake zargi da kashe ‘yarta ya sha zuwa gidansu yana neman ganin Ummita, amma ba ta son fitowa.

Ta ce a ranar da lamarin ya faru, É—an Chinan da ake zargi ya sake zuwa gidan da daddare inda ya yi ta buga musu kofa, abin da ya tilasta wa mahaifiyar bude masa kofa, don jin abin da ke tafe da shi.

Uwar ta ce Mista Geng ya bangaje ta, ya kutsa kai cikin dakin Ummita, kuma da ganin ta sai ya zare wuka ya yi ta caka mata.

More News

An sake gano gawar wani shugaban Fulani da ya É“ata a jihar Filato

An gano gawar wani Arɗon Fulani, Umar Ibrahim da ya ɓace a cikin wata rijiya dake kauyen Jokom a ƙaramar hukumar Mangu ta...

An kama Æ´an kungiyar IPOB 18 da ake zargi da kisan Æ´an sanda

Rundunar yan sandan jihar Imo ta kama mutane 18 da ake zargi da zama yan kungiyar IPOB da suke da hannu a kisan Æ´an...

Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da zaɓen gwamnan jihar Sokoto

Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja ta tabbatar da zaɓen, Ahmed Aliyu a matsayin gwamnan jihar Sokoto. Rukunin alkalan kotun su uku sun yi watsi da...

Kotun ɗaukaka ta soke zaɓen shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna

Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja, ta soke zaɓen kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman. Alkalan kotun uku sun bayar da umarni da a sake...