Kawo Yanzu An Kwaso Yan Najeriya 1984 Daga Sudan

Kawo yanzu yan Najeriya 1984 aka kwaso daga Sudan inda rikici ya barke a tsakanin jami’an sojan kasar.

Hukumar NIDCOM dake kula da yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ita ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar.

Sanarwar ta ce rukuni na 11 na yan Najeriya da suka haɗa da ƙananan yara 11 da kuma manyan mutane 117 sun sauka a filin jirgin saman Abuja a cikin jirgin kamfanin Tarco Airline da ya ɗebo su daga garin Port Sudan.

Hukumar ta ce kawo yanzu ba a samu asarar ran ko mutum guda ba a cikin yan Najeriya da ake kokarin kwaso wa daga kasar ta Sudan.

More from this stream

Recomended