Ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar kyamar baƙi a wasu sassan Afirka ta Kudu, lamarin da ya sa hukumomi suka jibge jami’an tsaro saboda fargabar barkewar rikice-rikice.
Shugaban ƙasar, Cyril Ramaphosa, ya bukaci masu zanga-zangar su guji tashin hankali tare da gudanar da zanga-zangar cikin lumana ba tare da tsoratar da jama’a ba.
Zanga-zangar na da nasaba da wa’adin da wasu ƙungiyoyi suka bai wa baƙin da ba su da takardun izinin zama a kasar su fice.
Lamarin ya haddasa fargaba tsakanin baki ‘yan Afirka da ke zaune a Afirka ta Kudu, yayin da wasu kasashe ke ci gaba da bibiyar halin da ake ciki.
An Jibge Jami’an Tsaro Yayin Da Zanga-Zangar Kyamar Baƙi Ke Ci Gaba A Afirka Ta Kudu

