Sojoji Sun Hallaka ’Yan Bindiga Biyu a Kogi, Sun Ƙwato Harsasai 5,000



Dakarun rundunar sojin Najeriya ta 12 Composite Brigade sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da ƙwato makamai da dimbin alburusai a wani samame da suka kai dajin Edimogbo, da ke Ƙaramar Hukumar Igalamela/Odolu ta Jihar Kogi.

Mukaddashin mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Talata.

Ya ce an gudanar da aikin ne a ranar 3 ga Nuwamba, 2026, bayan wani samamen da sojojin suka kai maboyar waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a dajin a ranar 2 ga Nuwamba.

A cewarsa, samamen na biyu ya mayar da hankali ne kan bin sawun waɗanda suka tsere a yayin artabun farko da kuma share sauran maboyar da ake zargin ’yan ta’addan na amfani da su.

Kayayyakin da sojojin suka ƙwato sun haɗa da bindigogin AK-47 guda biyu, harsasai bakwai na bindiga, alburusai 438 masu nau’in 7.62mm x 54, da kuma alburusai 4,725 masu nau’in 7.62mm Special.

Sauran kayayyakin sun haɗa da jakunkunan ɗaukar alburusai guda biyu, wayoyin hannu guda biyu da kuma na’urar cajin waya (power bank) guda ɗaya.

Rundunar sojin ta ce wannan nasara ta ƙara ƙarfafa ƙudurinta na ci gaba da matsin lamba kan masu aikata laifuka, kare rayuka da dukiyoyin al’umma, da kuma dawo da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a faɗin Jihar Kogi.

Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin na ci gaba da sintiri da mamaye yankin, yayin da ƙwarin gwiwarsu da ƙwarewarsu wajen gudanar da ayyukan tsaro ke ƙaruwa.

Rahoton ya kuma bayyana cewa dakarun rundunar ta 12 suna haɗin gwiwa da rundunar ’yan sandan Jihar Kogi da sauran hukumomin tsaro domin ƙarfafa yaƙi da masu garkuwa da mutane a sassan jihar.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...