Ƴan Sanda Sun Bankado Masana’antar Buga Kuɗaɗen Dala na Jabu a Ondo

Muhammadu SabiuHausa54 minutes ago



Rundunar ’yan sandan Jihar Ondo ta bankado wani wurin da ake zargin ana ƙera jabun kuɗaɗen dalar Amurka a Ƙaramar Hukumar Odigbo, inda ta kama mutum guda tare da ƙwato buhuna uku cike da takardun dalar Amurka da ake zargin na bogi ne.

Rundunar ta ce jami’anta sun gudanar da samamen ne a ranar 29 ga Oktoba a ƙauyen Kiniso, kusa da Ajue, bayan gudanar da bincike kan ƙorafin wani mutum da ya ce wasu mutane biyu sun damfare shi da jabun daloli yayin musayar kuɗi.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abayomi Jimoh, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

A cewar sanarwar, mutumin da ya kai ƙorafin mai suna Yusuf Nasiru, ya shigar da ƙara a ranar 28 ga Oktoba, inda ya ce wasu mutane biyu, Peter Desmond da Olami Toro, waɗanda ke zaune a Ode-Irele, sun je shagonsa a ranar 25 ga Oktoba domin musanya dalar Amurka da naira.

Jimoh ya ce Nasiru ya miƙa musu dala 6,000, wadda darajarta ta kai kusan naira miliyan 8.6.

Sai dai yayin da yake jiran a ba shi nairorin, waɗanda ake zargin sun dawo masa da dalolin, suna cewa ba su da isassun kuɗin da za su kammala cinikin, sannan suka bar wurin.

Sanarwar ta ce daga baya Nasiru ya binciki kuɗin da suka dawo masa da su, inda ya gano cewa jabun daloli ne, lamarin da ya sa ya kai ƙara ga ’yan sanda.

Bayan samun ƙorafin, jami’an rundunar daga hedikwatar ’yan sanda ta Okitipupa sun fara bincike cikin sirri, inda suka yi amfani da bayanan sirri da kuma na’urorin bin diddigi wajen gano ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Peter Desmond, a ƙauyen Kiniso.

Rundunar ta ce jami’an sun kai samame wurin da ake zargin maboyarsu ne a ranar 29 ga Oktoba, bisa bayanan da suka samu daga wasu mazauna yankin.

A yayin samamen, an kama mutum guda, yayin da sauran mutanen da ke cikin gidan suka tsere ta katangar gidan.

Binciken da jami’an suka gudanar a wurin ya kai ga gano buhuna uku cike da takardun dalar Amurka da ake zargin na bogi ne, tare da wani ƙaramin akwati na katako. An kwashe kayayyakin zuwa hannun ’yan sanda domin su zama hujjojin bincike.

Kakakin rundunar ya ce wanda aka kama ya bayar da wasu bayanai masu amfani da ke taimaka wa jami’an wajen ci gaba da bincike.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Felix Ohagwu, ya bayar da umarnin zurfafa bincike domin gano tare da kama sauran mutanen da ake zargin suna da alaƙa da wannan harkar.

Rundunar ta ce za ta kuma binciki girman wannan zargin damfarar jabun kuɗaɗen tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi ya fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Haka kuma, rundunar ta gargaɗi jama’a da su guji mu’amalar musayar kuɗaɗen waje da mutanen da ba a tantance ba, musamman cinikin da ake gabatarwa da tayin riba mai yawa fiye da yadda aka saba.

Ta kuma buƙaci jama’a su riƙa tantance sahihancin kuɗaɗen waje kafin karɓarsu, tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...