2027: Ɗan Obasanjo Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tazarcen Tinubu

Muhammadu SabiuHausa34 minutes ago



Olujuwon Obasanjo, ɗan tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya shiga ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement a matsayin mai ba ta shawara ta musamman kan harkokin siyasa, inda ya yi alƙawarin mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin sake zaɓensa a shekarar 2027.

Olujuwon ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai hedikwatar ƙungiyar da ke Abuja ranar Laraba, inda mai gudanar da ƙungiyar na ƙasa, Sunday Asuku, ya tarbe shi.

Bayan isarsa, an zagaya da shi cikin hedikwatar domin ya fahimci yadda ƙungiyar take gudanar da ayyukanta da tsarin tafiyarta.

Da yake bayyana jin daɗinsa kan naɗin da aka yi masa, Olujuwon ya yaba wa ƙungiyar bisa ƙoƙarinta na wayar da kan al’umma, tattara magoya baya daga tushe da kuma tallata ayyukan gwamnatin Tinubu.

Ya ce ya daɗe yana bibiyar ayyukan ƙungiyar, kuma ya gamsu da irin ƙoƙarin da take yi, yana mai cewa a shirye yake ya ba da gudummawarsa wajen cimma manufofinta da kuma tabbatar da wa’adin mulkin Tinubu na biyu.

A kalamansa, ya ce: “Shugaba Tinubu ya fara mulkinsa da kyakkyawan tsari, don haka ya zama wajibi ’yan Najeriya, musamman matasa, su haɗa kai domin ci gaba da sauye-sauyen da ake yi da kuma tabbatar da dorewar shugabanci.

“Haka kuma, za ku lura cewa ƙasar ta samu ci gaba a wasu fannoni, ciki har da biyan albashi, bunƙasa ababen more rayuwa da samar da damar zuba jari. Ina ganin ya kamata a kiyaye nasarorin da aka samu.”

Olujuwon ya bayyana kwarin gwiwar cewa ci gaba da goyon bayan Tinubu zai ba gwamnatinsa damar ƙarfafa nasarorin da ta samu tare da samar wa ’yan Najeriya ƙarin alfanun dimokuraɗiyya.

Ya kuma bayyana cewa ya kasance ɗan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tun shekarar 2014, yana mai cewa ’yan iyalinsa suna da ’yancin bin ra’ayoyin siyasa daban-daban ba tare da gaba ko ƙiyayya ba.

Ya ce: “Iyalinmu suna ba kowane ɗan gida damar kasancewa da ra’ayinsa na siyasa da kuma bin manufofinsa ba tare da wata gaba ba.”

A nasa jawabin, Asuku ya bayyana Olujuwon a matsayin gogaggen ɗan siyasa wanda ƙwarewarsa a harkokin jagoranci da shugabanci za ta ƙara wa ƙungiyar ƙarfi wajen tattara magoya baya.

Ya ce suna da tabbacin cewa ƙwarewarsa da fahimtarsa kan yadda ake gudanar da gangamin siyasa za su taimaka wajen faɗaɗa ayyukan ƙungiyar a faɗin ƙasar.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da ƙungiyoyin siyasa da jam’iyyun ƙasar ke fara shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, inda magoya bayan Shugaba Tinubu ke ƙara ƙaimi wajen tattara goyon bayan jama’a domin sake zaɓensa.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...