Shugaba Bola Tinubu Ya Bar Saudiyya Bayan Kammala Umarah

Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Tinubu, ya bar ƙasar Saudiyya bayan ya kammala ibadar Umarah.

Wani bidiyo da Olusegun Dada, mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, ya wallafa a ranar Laraba, ya nuna Tinubu yana yi wa jami’an Najeriya da na Saudiyya bankwana kafin ya hau jirgin sama.

Dada ya ce shugaban ya samu wata damar musamman ta shiga cikin dakin ka’aba mai tsarki da ke Makkah yayin ziyararsa.

A cikin wata sanarwa, Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban ƙasa, ya bayyana cewa jirgin Tinubu ya tashi daga   Filin Jirgin Saman Sarki Abdulaziz  da ke Jeddah da misalin ƙarfe 5:13 na yamma agogon Saudiyya.

Sanarwar ta ce:

“Mataimakin gwamnan yankin Makkah, Yarima Saud bin Mishaal bin Abdulaziz Al Saud; Jakadan Najeriya a Saudiyya, Ambasada Yakubu Gambo; da Babban Jakadan Najeriya, Ambasada Muazam Ibrahim Nayaya, sun raka shugaban ƙasar zuwa filin jirgin saman.

“Kafin tashinsa, Shugaba Tinubu ya yi gajeriyar ganawa da Mataimakin Gwamnan Makkah a Fadar Saukar Baki Ta Masautar Saudiya da ke filin jirgin saman.”

Tinubu ya isa Saudiyya ne a ranar 29 ga Oktoba.

Tun da farko, Onanuga ya bayyana a wata sanarwa cewa ziyarar za ta ba Tinubu damar yin nazari na tsakani, ibada, da addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali da ci gaban Najeriya.

Ya kuma ce shugaban ƙasar zai koma Najeriya bayan kammala aikin Umarah.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...