

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Garba Umar, ta soke zaɓen da aka yiwa Manjo Janar Nuhu Angbazo (mai ritaya) a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar ADC a Jihar Nasarawa. Kotun ta kuma hana shi ci gaba da ayyana kansa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen gwamna na shekarar 2027.
Haka ila yau, kotun ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da kada ta amince da Angbazo a matsayin ɗan takarar ADC har sai an bi umarnin da kotun ta bayar.
Tsohon Ministan Muhalli, Mohammed Hassan Abdullahi, ne ya shigar da ƙarar gaban kotun, Hassan na daga cikin waɗanda suka shiga zaɓen fidda gwanin tare da Angbazo da Sanata Mohammed Ogoshi Onawo mai wakiltar Nasarawa ta Kudu.
Kotun ta yanke hukuncin cewa zaɓen fidda gwani da ya samar da Angbazo a matsayin ɗan takara bai kammala ba saboda ba a haɗa sakamakon ƙaramar ghukumar Karu ba. Haka kuma, waɗanda ake ƙara sun amince cewa ba a gudanar da zaɓe a Karu ba.
A cewar kotun, idan ba a yi zaɓe a Karu ba, to ba za a iya cewa an kammala zaɓen fidda gwanin yadda ya kamata ba. Saboda haka, dole ne a gudanar da zaɓe a Karu kafin a sami sahihin ɗan takarar jam’iyyar.
Saboda haka, kotun ta umarci ADC da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani a gundumomi 11 na Ƙaramar Hukumar Karu. A farko dai, mai shigar da ƙara ya nemi a ƙirga ƙuri’un Karu da aka yi watsi da su kuma a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen, amma kotun ta zaɓi a sake gudanar da zaɓen a yankin.