
Kwamitin rage cunkoson gidajen gyaran hali na jihar Adamawa ya saki fursunoni 55 tare da bayar da belin wasu 51 bayan ziyarar da ya kai gidan gyaran hali na Yolde Pate da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.
An gudanar da ziyarar ne ranar Laraba karkashin jagorancin Mai Shari’a Hafsat Abdulrahman, wadda ita ce babbar alkalin jihar.
Kwamitin ya fi duba kananan laifuka da rikice-rikicen farar hula da kananan sace-sace, yayin da ake barin manyan laifuka kamar kisan kai, fyade da laifukan kungiyoyin daba ga kotunan da suka dace domin ci gaba da shari’a.
A yayin ziyarar, Mai Shari’a Hafsat ta bai wa wata fursuna da ta haifi diya mace a lokacin da take tsare kayayyakin taimakon haihuwa. Shugaban iyalin jaririyar ya sanya mata suna Hafsat domin girmama babbar alkalin.
Haka kuma, babbar alkalin ta ba fursunonin da aka saki kudin mota domin komawa jihohinsu, ciki har da Bauchi, Yobe da Gombe.